Kamfanin sadarwa na MTN A Najeriya, ya shigar da kara akan cinsa tarar fiye da dala biliyan daya da aka yi
Sunday, 4 August 2019
Comment
Kamfanin sadarwa na MTN A Najeriya, ya shigar da kara akan cinsa tarar fiye da dala biliyan daya da aka yi
Kamfanin na MTN wanda daya ne daga cikin manyan kamfanonin sadarwa a cikin kasar ta Najeriya ya bukaci kotun daukaka kara akan harkokin haraji ta sake bitar ko ya cancanci ya biya tarar Naira biliyan 330 ( wanda ya yi daidai da dalar Amurka biliyan 1.1)
Tun da fari an ci kamfanin na MTN tarar naira tiriliyan 1.04 ne saboda ya ki ya rufe layukan waya har miliyan biyar wadanda ba su yi wa katinan nasu rijista ba, dai dai bayan tattaunawa ta samu an rage yawan kudaden da aka ci tararta.
Kamfanin ya bukaci ganin an yi bitar harajin ne dai bayan da aka sami sabani a tsakaninsa dahukumar tattara haraji ta kasar Najeriya, akan kudaden tafiyar da kamfanin
Mai Magana da yawun kamfanin ya ce; A halin yanzu suna sauraronhukuncin da kotun za ta yanke dangane da batun tarar, da ka iya zama zakaran gwajin dafi akan kamfanonin kasashen waje da suke da rijista a cikin Najeriya.
IsiyaSy✍️
Kaduna Press

0 Response to "Kamfanin sadarwa na MTN A Najeriya, ya shigar da kara akan cinsa tarar fiye da dala biliyan daya da aka yi"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?